Sanata Barau Ya Karɓi Tawagar Masu Ruwa da Tsaki daga Bichi
Daga: Mannir H A Kabo
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi baƙuncin tawagar masu ruwa da tsaki na siyasar Rabiu Sulaiman Bichi daga Ƙaramar Hukumar Bichi, waɗanda suka kai masa ziyarar girmamawa a gidansa dake Abuja.
Tawagar, wadda ta ziyarce shi a daren Alhamis, ta kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyyar APC na Kano ta Arewa, Hon. Abdullahi Magaji Lamba.
A jawabin da Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na sada zumunta bayyana cewa tawagar ta zo ne ƙarƙashin jagorancin siyasar Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, Babban Daraktan Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (HJRBDA).
Sanatan Ya yabawa Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen jagora mai himma wajen bunƙasa jam’iyyar APC da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta.
A nasa jawabin, mai magana da yawun tawagar, Kuma Mataimaki na musamman ga Injiniya Rabiu Bichi, Hon. Zubairu Hamza Pasha Bichi, ya ce sun kai ziyarar ne da cikakken sani da amincewar Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi domin nuna godiya ga Sanata Barau, tare da sake tabbatar masa da cikakken goyon bayansu.
Sanata Barau, a nasa martanin, ya bayyana farin cikinsa da ziyarar, yana mai cewa irin wannan haɗin kai da juna na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban jam’iyya da kuma al'umma.
Sanatan Ya Kara da miƙa godiyarsa ga Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, Hon. Abdullahi Magaji Lamba, Hon. Zubairu Hamza Pasha da dukkan mambobin tawagar bisa amincewa, haɗin kai da kuma goyon bayan da suke ci gaba da nuna masa.










