Friday, July 17, 2026

SHUGABAN RIKO NA KWALEJIN SHARI'A DA ADDININ MUSULINCI TA AMINU KANO (AKCILS) DA AKAFI DANI DA LEGAL, YA NEMI MAJALISSAR DOKOKIN KANO TA AMINCE KWALEJIN TA ZAMA CIKAKKIYAR KWALEJIN ILIMI

Shugaban riƙon Kwalejin  ta Aminu Kano (AKCILS), Dakta Ali Tamasi Mu'az, ya buƙaci Majalisar Dokokin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudirin mayar da kwalejin zuwa cikakkiyar Kwalejin Ilimi.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar Kwamitin Ilimi Mai Zurfi na majalisar, inda ya ce NCCE ta ƙara darusan NCE na kwalejin daga 32 zuwa 52, yayin da NBTE ta ɗaga shirye-shiryen Diploma na Law da Shari'a zuwa Babbar Diploma.

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Ilimi Mai Zurfi, Dakta Ali Lawan Alasan, da Shugaban Masu Rinjaye, Lawan Hussaini Dala, sun tabbatar da goyon bayan majalisar ga ci gaban kwalejin.

– Abbas Musa Sheka

Mannir H Kabo 


No comments: