Sunday, July 12, 2026

Jaridar ƙasar Iran ta wallafa sunayen Trump da shugabannin Turai a jerin waɗanda ake son ɗaukar fansa a kansu

 Jaridar ƙasar Iran ta wallafa sunayen Trump da shugabannin Turai a jerin waɗanda ake son ɗaukar fansa a kansu



Wata jaridar masu ra'ayin mazan jiya a Iran mai suna Hamshahri ta wallafa jerin sunayen wasu fitattun shugabannin duniya da ta ce suna cikin waɗanda za a ɗauki fansa a kansu sakamakon kisan tsohon Jagoran Addini na Iran, Ayatullah Ali Khamenei.


Rahotanni sun ce Ali Khamenei ya rasu ne bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, wadda ita ce ranar farko ta yaƙin Gabas ta Tsakiya.


Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansa, inda a saƙonsa na farko bayan jana'izar mahaifinsa ya ce, "Ɗaukar fansa shi ne muradin al'ummarmu, kuma dole ne a aiwatar da shi."


Ya kuma ce waɗanda sunayensu ke cikin jerin ba za su samu mutuwar lumana ba.


Jaridar Hamshahri, wadda hukumomin birnin Tehran ke bugawa, ta fitar da hotunan shugabannin ƙasashe 13 tare da saƙon Mojtaba Khamenei. Sai dai sabon jagoran bai bayyana sunayen mutanen da Iran ta ce ta sanya a cikin jerin ba, kuma babu wata shaida da ke nuna cewa gwamnatin Iran ta amince da jerin sunayen da jaridar ta wallafa.


Daga cikin waɗanda ke cikin jerin akwai Shugaban Amurka Donald Trump, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Firaministan Birtaniya Keir Starmer, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Firaministar Italiya Giorgia Meloni da kuma shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz.


A lokacin yaƙin, Iran ta zargi wasu ƙasashen Turai da kin yin Allah wadai da hare-haren da aka kai mata, tare da zarginsu da bai wa jiragen sojin Amurka damar amfani da sararin samansu.


Rahotanni sun kuma ce Mojtaba Khamenei bai fito bainar jama'a ba tun kafin fara yaƙin, kuma an ce ya samu raunuka a hare-haren da suka kashe mahaifinsa.


Rahoton Daily Nigerian Hausa 



No comments: