Sunday, July 12, 2026

Sojoji sunyi nasarar kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Yellow Danbokolo, daya daga cikin manyan abokan hulɗar Bello Turji.

 Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Yellow Danbokolo, daya daga cikin manyan abokan hulɗar Bello Turji.

Kachalla Yellow ya mutu ne bayan wani artabu tsakanin jami’an tsaron Zamfara da tawagarsa a yankin Shinkafi.

Kachalla Yellow Danbokolo ya shahara wajen jagorantar hare-hare, sace mutane domin karɓar kuɗin fansa da sauran ayyukan ta’addanci a yankunan Shinkafi, Sabon Birni, Isa, Goronyo da wasu sassan Arewa maso Yamma.




No comments: