Kisan uwa da yayan ta a Kano: Matashin da ake zargi ya ce boka ne ya sa shi ya aikata haka
Babbar kotun jihar Kano mai lamba ta 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Nasiru Saminu, ta ci gaba da sauraron shari'ar Umar Auwalu, Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu, waɗanda ake tuhuma da kisan Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci da ke Kano.
A zaman kotun da aka yi ranar Laraba, Umar Auwalu mai shekaru 23, yayin kare kansa, ya shaida wa kotu cewa shi kaɗai ne ya aikata kisan matar kawunsa Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida a watan Janairun 2026.
Ya ce wani boka kuma mai sayar da maganin gargajiya mai suna Thomas ne ya ba shi wani turare tare da umartarsa da ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka.
Umar ya kuma bayyana cewa sauran waɗanda ake tuhuma tare da shi, Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu, ba su da hannu a kisan. Ya ce ya ambaci sunayensu ne bayan da ya fuskanci azaba a hannun jami'an 'yan sanda bayan kama shi.
A ɓangaren masu gabatar da ƙara, lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata sun gabatar da jami'in binciken 'yansanda, Kofural Aliyu Jamilu, a matsayin shaida. Haka kuma lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma sun gabatar da shaidunsu a gaban kotu.
Mai Shari'a Nasiru Saminu ya ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga Yuli, 2026, domin ci gaba da karɓar shaidu da sauraron ɓangarorin shari'ar.
Ana zargin cewa a ranar 17 ga Janairu, 2026, an kashe Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida a gidansu da ke Dorayi Ciranci a Kano. Bayan binciken da 'yan sanda suka gudanar, an kama Umar Auwalu tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a kisan.
Tun da farko an gurfanar da waɗanda ake zargin a Kotun Majistare ta Nomansland kan tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da haɗa baki, kisan kai, fashi da makami da kuma fyade. Daga baya, bayan nazarin da Daraktan Hukumar Gurfanar da Masu Laifi (DPP) ya yi, an mayar da shari'ar Babbar Kotu inda aka sake gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda tara.
Yayin da Umar Auwalu ya amsa wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa, sauran waɗanda ake tuhuma biyu sun musanta aikata dukkan laifukan da ake zarginsu da su.
![]() |
| Daily Nigerian Hausa |

No comments:
Post a Comment