Jam’iyyar ADC Bangaren Nafiu Bala Ta Kammala Loda Sunayen ’Yan Takararta a Tsarin INEC Domin Zaɓen 2027
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) bangaren Hon. Nafiu Bala Gombe ta sanar da cewa ta kammala loda sunayen ’yan takararta na shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa da kuma ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa a shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da Hon. Nafiu Bala Gombe, wanda ya bayyana kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, ya fitar a ranar 12 ga Yuli, 2026, ya ce matakin ya nuna jajircewar bangarensa wajen kare muradun waɗanda suka kafa jam’iyyar da kuma tsofaffin mambobinta, duk da abin da ya kira ƙalubalen da ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya.
Sanarwar ta ƙara da cewa bangaren ADC na ci gaba da tsayawa kan manufarsa ta tsayar da nagartattun, ƙwararru kuma masu kishin jama’a a matsayin ‘yan takara domin samar da shugabanci nagari, inganta kyakkyawan tsarin mulki da kuma dawo da fata ga al’ummar Najeriya.
![]() |
| Kabo Reporters |

No comments:
Post a Comment