Friday, January 2, 2026

GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA FALLASA ASIRIN MINISTAN ABUJA NYESOM WIKE

GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA FALLASA ASIRIN MINISTAN ABUJA NYESOM WIKE


Maigirma Gwamnan jihar mu na Bauchi Senator Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Daular Usmaniyyah) ya fallasa asiri na makircin da Ministan Abuja Nyesom Wike yake kulla masa da jihar Bauchi gaba daya


Maigirma Gwamna yayi wannan fallasa ne a cikin shirin Sunrise Daily na Channels TV dazu da safe, yace akwai wanda yake shirya min makirci, kuma na san shi, shine Ministan Abuja na yanzu Nyesom Wike, ya fada wa duniya cewa zai kunna wuta a jihata na Bauchi


Kauran Daular Usmaniyyah yaci gaba da cewa; na fahimci Wike ne yake bada umarni wa hukuma irin na EFCC wajen batani, yana bawa mutane cin hanci, yana sayar da filayen Abuja yana amfani dasu wajen cimma burinsa, ba sabon abu bane a gareni saboda na taba rike mukamin Ministan Abuja na shekaru 6 na san komai


Gwamnan Bauchi yaci gaba da cewa; yana da hujjoji daga majiyarsa na sirri dake EFCC wanda suka tabbatar masa da cewa Wike ne yake tsara duk abinda yake faruwa da ‘yan adawar siyasa a Nigeria


Kaura yace tsohon Accountant General dinsa na jihar Bauchi yaci amanata, ni na kaishi Kotu da kaina domin a masa hukunci, daga bisani Kotu ta bada belinsa, to a yanzu Wike ne yake aiki dashi a Kotu wajen bada shaida na karya akan mukarrabaina da aka kama


A matsayina na Gwamna wanda na rike manyan mukamai tun daga Sanata har Minista, ina shugaban al'ummah ta ya zai kasance ina daukar nauyin ta'addanci, ana min wannan sharri ne saboda ina cikin manyan 'yan adawa


Zan bi duk matakan da suka dace domin na kare kaina, na rubuta wa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya takardan korafi, tare da sanar da hukumomin tsaro, kuma zan kai korafina zuwa ga hukumonin Majalisar dinkin duniya, inji Maigirma Gwamna


Sannan Gwamna Bala yace Shugaban Kasa Tinubu yana kewaye da 'yan daba, 'yan damfara wadanda suke son ha||akashi a siyasance irinsu Wike


Muna rokon Allah Ya kare jihar Bauchi daga wadanda suke neman jingina mana ta'addanci, Allah Ya sa mugun nufinsu ya kare a kansu da iyalansu kadai.


 


DA DUMI-DUMINSA:

 Jerin Sanatoti Hudu Da 'Yan Majalisun Tarayya Duda Shida Da Suka Sanar Da Komawarsu Jam'iyyar Hadaka Ta ADC A Hukumance

SENATE

1. Sen. Enyinnaya Abaribe. Abia South Senatorial District

2. Sen. Ireti Kingibe. Federal Capital Territory (FCT)

3. Sen. Victor Umeh. Anambra Central Senatorial District

4. Sen. Tony Nwoye. Anambra North Senatorial District. 

🏛️ HOUSE OF REPRESENTATIVES

1. Hon. Seyi Sowunmi. Ojo Federal Constituency, Lagos State

2. Hon. Oby Lilian Orogbu. Awka North/Awka South Federal Constituency, Anambra State

3. Hon. George Adegeye. Amuwo-Odofin Federal Constituency, Lagos State

4. Hon. Harris Uchenna Okonkwo. Idemili North/Idemili South Federal Constituency, Anambra State

5. Hon. Murphy Osaro Omoruyi. Egor / Ikpoba-Okha Federal Constituency, Edo State

6. Hon. Afamefuna Ogene. Ogbaru Federal Constituency, Anambra State.



 

GWAMNAN JOS YA YANKI KATIN JAM'IYYAR APC

 Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya yanki katin zama dan jam'iyyar APC a yau Juma'a bayan ficewa daga PDP




Thursday, January 1, 2026

BARKA DA SABUWAR SHEKARA DAGA KABIRU GETSO

HON. KABIRU GETSO HARUNA 

 Tsohon shugaban Hukumar bada tallafin karatu ta jihar Kano Honourable Kabiru Getso Haruna Kuma Mai bawa Gwamnan jihar Kano shawara akan harkokin samarda Aiyuka.

 yana Taya alummar Karamar Hukumar Gwarzo da jihar Kano murnar shaida sabuwar shekara.

Mr. Getso ya aike da wannan Sako ta hannun PA dinsa Comrade Hafiz Ayuba Kutama.

Inda sakon ke dauke da wata Kalmomin barkwanci da aika Sako cikin hikima. 

Inda Mr Getso yace " Duk abin da kake so a rayuwa, wasu mutane ma za su so shi. Ka yarda da kanka Kuma ka yarda da ra'ayin cewa kana kan daidai da wannan hakki. Ina so nayi amfani da wannan damar don yi wa mutanen kirki na Karamar Hukumar Gwarzo da Jihar Karo fatan alheri da wadata a Sabuwar Shekarar 2026 ina fatan ta kasance maku cikin  farin ciki, nasara, zaman lafiya, da albarkatu marasa adadi. Barka da Sabuwar Shekara!"...